Gwamnan jihar Nasarawa, Umar Tanko Al-Makura

A jiya Talata, matasa a sansanin ‘yan gudun hijira a karamar hukumar Obi a jihar Nassarawa sun yi wa gwamnan jihar Tanko Almakura  tare da tawagar shi ruwan duwatsu.

Gwamnan ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijirar ne domin duba yanayin tsaro a sakamakon hari da makiyaya suka kai da ya haddasa rasuwar mutane 32 a ranar Lahadin da ta gabata.

A yayin da gwamnan ke kokarin yin jawabi ga ‘yan gudun hijirar ne wasu matasa a sansanin suka fusata suka kuma fara wake-wake, lamarin da ya sa gwamnan ya bar wajen.

Daga nan lamarin ya ta’azzara, inda matasan suka fara jifan tawagar gwamnan da duwatsu, wanda ya sa ‘yan sanda suka yi amfani da barkono tsohuwa wajen tarwatsa su.

Almakura dai ya ce hakan ya faru ne sakamakon irin kalubalen da ‘yan gudun hijirar ke fuskanta.

“Yanayin mutanen ya bayyana ne ganin yadda suke fuskantar kalubale kuma dole mu bi a hankali wajen shawo kan lamarin”.

“Ci gaba da yi musu jawabi a lokacin ba zai haifar da da mai ido ba, saboda haka sai muka janye,” inji Almakura.

Gwamnan ya shawarci shuwagabannin al’ummar da su gargadi mutanensu game da daukar doka a hannu.

“In dai za ku dauki doka a hannunku, to za a kyale ku da matsalolin ku,” a cewar gwamna Almakura.

Ya bada umurni wa shugabannin kananan hukumomin da abin ya shafa da su
kawowa ‘yan gudun hijiran kayan agaji.

LEAVE A REPLY