A sakamakon wani tashin hankali da ya biyo bayan cinnawa wasu makiyaya 7 wuta suka kone kurmus, ya sanya a ranar laraba Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya sanya dokar hana fita a yankin karamar hukumar Gboko.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Moses Yamu, ya tabbatar da kai wannan farmaki ga Fulani makiyaya, inda yace,wasu fusatattun matasa ne suka kai wannan hari.

“Abin babu kyan gani a babbar tashar mota ta garin Gboko, cikin gaggawa ‘yan sanda suka hallara a wannan waje domin bayar da kariya da kuma kwantar da tarzoma, da zuwan ‘yan sanda wajen sun tarar da gawar mutum 7 wanda dukkaninsu maza ne, har ya zuwa wannan lokaci bamu kai ga gano ko sunayensu ba, balle inda suka fito, amma dai mun san Fulani ne, an kai musu hari, aka kashe su, sannan aka cinnawa gawarwakinsu wuta, a cikin tashar motar Gboko” A cewar Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai.

Sai dai kuma, DAILY NIGERIAN ta gano cewar, mutanen da aka kashe din, Fulani ne da ke neman tsira zasu tsallaka jihar Kogi ko Taraba wannan al’amari ya rutsa da su.

A cewar mai magana da yawun Gwamnan jihar Binuwa Tahav Agerzua, yace, Gwamnan Samuel Ortom ya bukaci jami’an tsaro da su sanya ido a lungu da sako na yankin karamar hukumar Gboko domin dawo da doka da oda.

Sannan kuma, Gwamnan ya bukaci jama’a da su kiyaye wannan doka ta ba shiga ba fita da aka sanya a yankin domin dawo da zaman lafiya a yankin.

Sai dai kuma, tuni ‘yan sanda suka yi samame inda suka kama wasu matasa da ake kyautata zaton suna da hannu a wannan tarzoma da ta barke a garin na Gboko.

Haka kuma, wadan da ake tsare da su, suna baiwa ‘yan sanda hadin kai wajen samun bayanai kan wannan lamari, a cewar Kwamishinan ‘yan nasandan jihar Mista Owoseni.

“Abin da matasan suka yi tsabar rashin Imani ne, wanda babu wani addini ko kabila da zasu goyi bayan aikata ta’addanci irin wannan”

“A sabida haka, duk wadan da aka samu da hannu cikin wannan mugun aikin ta’addanci zasu fuskanci hukunci mai tsanani”

 

 

LEAVE A REPLY