Matasa hudu da ake zargi da yiwa yarinya fyade

 

Hassan Y.A. Malik

Rundunar jami’an tsaro na sibil difens reshen jihar Neja sun kama wasu maza 4 bisa zargin yi wa budurwa ‘yar shekaru 19 fyade.

Wadanda ake zargin sun hada da: Muhammad Surajo mai shekaru 21, Shafi’i Muhammad mai shekaru 19, Muhammad Abubakr mai shekaru 19, sai Musa Liya mai shekaru 16 da haihuwa.

An kama wadannan mutane a garin Barikin Sale, cikin karamar hukumar Chanchaga ta jihar Neja.

Kwamandan rundunar, Philip Ayuba, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai yaua a garin Minna, inda ya kara da cewa, wadanda a ke zargi sun amsa laifinsu.

Kwamandan na sibil defens ya ci gaba da cewa, wadanda a ke zargin sun fadi cewa sun hada kai wajen aikata fyaden ne bayan da yarinyar ta ki amincewa da bukatar daya daga cikinsu na ya yi lalata da ita.

Tuni dai aka mika wadanda a ke zargi zuwa ga ma’aikatar shari’a ta jihar don a tabbatar musu da hukunci daidai da laifinsu.

Philip Ayuba ya tabbatarwa da manema labarai cewa za su bi wannan shari’a har sai an tabbatar da adalci ga wacce aka zalunta. Haka kuma ya gargadi ‘yan mata da su guji zirga-zirga a kan hanyar da babu jama’a sosai.

LEAVE A REPLY