Marigayiya Binta Safiyanu

Da sanyi safiyar ranar talatar jiya ne, Binta Safiyanu, matar dan majalisa mai wakilar Musawa a majalisar dokokin jihar Katsina, Yunusa Jikamshi ta rigamu gidan gaskiya, bayan da ta sha wani maganin gargajiya domin karin ruwan nono.

Rahotanni sun tabbatar da cewar, Binta, wadda ta haifi yara shida, ta rasu ne bayan da ta sha magnin karin ruwan nono domin shayar da jariranta, sati guda bayan da ta haifi ‘yan tagwaye.

Bayan Binta Safiyanu ta haifi ‘yan tagwaye, ruwan nonon da take da shi ya kasa wadatar da jariran da ta haifa, a sabida haka kishiyoyinta suka bata maganin gargajiya da zai kara mata yawan ruwan nono.

Wani na kusa da ita yace, kishiyoyinta ne suka bata maganin tare da tabbatar mata cewar zai kara mata yawan ruwan nono idan tayi amfani da shi.

Wata majiyar kuma ta bayyana cewar, ita mai jegon ce ta bukaci wata da ake kira Sakina da ta hada mata maganin ta sha, mintoci kadan Binta ta fara hararwa bayan ta sha maganin.

An garzaya da ita asibitin kwararruna garin Musawa inda aka tabbatar da rasuwarta, tuni dai aka yi mata sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

uni dai aka kai wannan batu gaban rundunar ‘yan sanda ta karamar hukumar Musawa, inda daga nan aka mika batun zuwa ga sashin binciken musamman na rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina domin yin binccike kan lamarin.

Tuni dai ‘yan sanda suka garkame Sakina, wadda tun farko ita ce ta baiwa Binta maganin da ta sha.

A alokacin da aka tambayi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Isah gambo ya tabbatar da wannan labari, ya kara da cewar, tuni ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike akan hakikanin abinda ya kashe Binta.

Haka kuma, har yazuwa lokacin hada wannan rahoto bamu samu jin ta bakin dan majalisar ba domin jin abinda zai ce.

LEAVE A REPLY