Daga Hassan Y.A. Malik

Kotu ta tasa keyar wata mace mai shekaru 24 da haihuwa zuwa gidan yari bayan da aka sameta da laifin da a ke zarginta da shi na lalata wani yaro dan shekara 16 da haihuwa sanadin da ya sanya ta kawar masa da samartaka.

Wandera, wacce ‘yar asalin kasar Kenya ce ta gurfana a gaba kotu ne bisa zarginta da kulla alakar soyayya da wani yaro mai karancin shekaru, alakar da daga baya ta rikide ta koma ta lalata, kuma an samu shaidu da dama da suka tabbatar da faruwar bata yaron da Wandera ta yi.

Mai shigar da kara, Nyakundi Mukaya ya gabatar da wata takardar asibiti ga kotu don tabbatar mata da cewa lalle Wandera na mu’amalar banza da yaron.

Mai shigar da karar ya ci gaba da fadawa kotu cewa, yaron ya ajiye batun karatunsa ya kuma koma gidan Wandera ya tare na tsawon watanni 4 har sai da ‘yan sanda suka ceto shi.

Wannan lamari dai ya faru ne tun  a shekarar 2016 zuwa 2017, inda a ranar 7 ga watan Yuli, 2017 ne ma ‘yan sanda suka yi nasarar karbo yaron daga hannun Wandera kuma nan take aka wuce da shi wa gidan gyatta tarbiyya kafin daga bisani a mika shi a hannun iyayensa.

Iyayen yaron sun koka da cewa tun bayan da yaronsu ya hadu da Wandera sai ya daina son makaranta gaba daya.

Wandera ta bayyana cewa ko a lokacin da ta hadu da yaron a watan Afrilun shekarar 2016 a garin Kondela kasurgumin dan shaye-shaye ne kuma baya kama da yaro karami a yanayin mu’amala da siffar jikinsa.

Ta ce, “Mun hadu da shi ne a wata mashaya inda ya nemi da ya saya min giya ni kuma na amince.

“Sam a lokacin ba ya kama da karamin yaro sakamakon yanayin sumar da ya bari (dada) da kuma kasancewarsa mai sana’ar acaba da a can Kenya a ke kira da boda-boda.

“Sai a yanzu ne da ya aske sumar da ke kansa na ke masa kallon yaro karami,” inji Wandera.

LEAVE A REPLY