Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta cafke wata mace da ta sayar da danta da ta haifa akan Naira 300,000.

Kakakin rundunar ‘yan sandan na Enugu, SP Ebere Amaraizu ne ya fitar da sanarwa dauke da wannan batu a ranar Asabar din da ta gabata.

SP Ebere ya ce, ‘yan sanda sun fara bincike don gano gaskiyar lamarin ne a ranar 3 ga watan Mayu bayan da suka kama 1 daga cikin masu sayen yaron.

Mahaifiyar yaron da aka sayar din, wata mace da aka bayyana sunanta da Nwanneka Ezechi, mai shekaru 30 da haihuwa, wacce ‘yar kauyen Akama Oghe ce da ke karamar hukumar Ezeagu ta jihar Enugu ta samu jaririn daga wata alaka da wani saurayinta.

Bayan samun juna biyun nata ne sai Nwanneka ta sulale ta bar gidan iyayenta zuwa wata maboya.

Nwanneka ta bayyanawa ‘yan uwanta cewa ta haifi da namiji a watan Nuwamban 2017 amma ba ta taba nuna musu dan da ta haifa din ba.
Sai dai bayan ‘yan uwanta sun gano inda ta ke kuma sun bincika basu ga dan da ta haifa ba, sai suka kai rahoto ga ‘yan sanda, inda ‘yan sanda kuma ba su yi wata-wata ba suka cafke Nwanneka.

Bayan tuhumar da aka yi wa Nwanneka sai ta bayyanawa ‘yan sanda cewa ta sayar da yaron ga wani Okechukwu Nyia da ke kauyen Akpasha da ke karamar hukumar Nkanu ta yamma akan kudi Naiara 300,000

Kakakin ‘yan sanda ya ce, zuwa yanzu dai ‘yan sanda na samun hadin kan wanda aka kama domin yana bayar da gamsassun bayanan wanda suka sayarwa da yaron.

LEAVE A REPLY