Daga Hassan Y.A.Malik

Mujallar 9News ta rawaito yadda wata mata mai dauke da juna biyu da fulani makiyaya suka yi wa fyade ta mutu a kan idon gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom.

Gwamnan wanda ya je ganin halin Lahaulan da wannan mata ke ciki, ya yi kira ga matasan jihar da su tashi tsaye wajen kare kansu daga hare-haren Fulani makiyaya.

Ya ce, bai kamata su ci gaba da zura idanu ba ana yi musu kisan kiyashi, saboda wani abu wai shi bin doka da oda.

Gwamnan ya jadaddawa matasan haka a ziyarar da ya kaiwa matar dake dauke da juna biyu da makiyayan suka yiwa fyade wanda ta cika akan idonsa a asibiti

Duk da yawan jami’an tsaron da gwamnatin Nijeriya ta tura zuwa jihar Binuwe, fulani makiyaya na ci gaba da kai hari da kisa a wasu kauyukan jihar, inda a baya-bayan ma sun kai wani harin da ya yi sanadiyyar rayuka da dama tare da kone gidaje sama da 50.

LEAVE A REPLY