Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osibanjo
Daga Hassan Y.A. Malik

A jiya Alhamis ne wani jirgin sama mai saukara ungulu dauke da mataimakin shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi saukar gaggawa ‘yan sakanni kadan bayan ya tashi sakamakon gaza cillawa sama da jirgin ya yi saboda matsala da ya samu.
Jirgin dai shi ne ya kai Osinbajon wajen taro yaye daliban makarantar daukar horo da ayyuka na hukumar kwastam, kuma bayan an kammala taron, jirgin ya yi yunkurin komawa da Osinbajo zuwa fadar shugaban kasa, amma sai jirgin bayan ya yunkura ya rabu da kasa, ya kasa cillawa ya yi sama zuwa matakin da zai iya tafiya, lamarin da ya sanya jirgin ya saki wani bakin hayaki mai kauri, alamar an takura shi.

A lokacin da abin ya faru a jiyan, babban hafsan sojin kasa na Nijeriya, Tukur Buratai da ba sojojin sama na Nijeriya, Sadique Abubakar sun bar wajen taron kenan ba da jimawa ba aka samu wannan matsalar.

Daga baya dai ala dole aka dauki Osinbajo a jerin gwanon motoci aka bar harabar kwalejin horar da jami’an kwastam din da ke a Gwagwalada, Abuja.

LEAVE A REPLY