Gwamnan jihar Katsina Alhaji AMinu Bello Masari

Mataimaki na musamman ga gwamnanjihar  Katsina kan harkokin addinai, Abdullahi Darma ya yi sanadiyar ajalin ‘yarsa, Aisha, ta hanyar murkusheta da mota a yayin da ya ke yin ribos.

Wannan lamari ya faru ne a gidan Malam Darma din da ke cikin garin Katsina, kuma Aisha ta rasu a nan take, kamar yadda wata majiya da ke kusa da iyalin Darma ta fada.

Malam Darma, ya tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari a shafinsa na facebook, kuma sanarwar tasa ta kawo dubunnan masu tausayawa a shafin nasa.

“Mintuna kadan da suka gabata na gamu da jarrabawa daga Allah, inda ina kokarin yin ribos da motata sai na murkushe tare da kashe ‘yata,” kamar yadda Malam Darma ya rubuta a shafinsa na facebook

LEAVE A REPLY