Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar jiya bai ji da dadi ba, yayin da mutane suka yarfa shi a bainar jama’a, bayan da yazo karbar mutane 4000 da zasu sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyarsa ta APC, inda a yayin taron aka nemi mutanan aka rasa.

Gwamna Badaru yaje karamar hukumar Birnin-Kudu ne a jihar domin ya karbi mutanan da zasu sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulkin jihar, sannan kuma ya kaddamar da wasu ayyukan raya kasa a yankin.

Taron dai dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Birnin Kudu da Buji, Injiniya Magaji Da’u Aliyu ne ya shirya shi domin ya raba kayan tallafi da kuma romon demokaradiyya ga al’ummar yankin da yake wakilta. A taron dai dan majalisar ya raba motoci da kaddamar da ginin hanya da kuma bayar da tallafin Naira miliyan 20 ga dalibai masu karatu a manyan makarantun ihar.

Danmalam Unguwar ‘Ya shi ne jagoran wadan da zasu sauya shekar daga PDP zuwa APC, an neme shi an rasa lokacin da aka dinga kiransa ya fito a madadin mutanan da zasu koma APC din, sannan babu ko mutum guda da ya fito da sunan zai sauya sheka.

Gwamna Badaru ya nuna rashin jin dadinsa kan wannan abu da ya faru a fuskarsa. Daga bisani ya kaddamar da ginin hanya daga Waurno zuwa Dankoshe, sannan kuma ya mikawa jagoran dalibai cakin miliyan 20 wanda dan majalisa Da’u Aliyu ya basu.

Sai dai mai baiwa Gwamnan shawara kan hulda da ‘yan jaridu Bello Zaki, yace Shugaban jam’iyyar APC na jihar shi ne kadai zai iya bayyana dalilin da ya sanya mutanan da za’a karba suka ki bayyana a yayin taron.

Jigawa State governor, Muhammed Badaru at Birnin Kudu Local Government Area

Premiumtimesng.com

LEAVE A REPLY