Sheikh Adam Al-Garkawy

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna a ranar Juma’a ta tabbatar da sace tare da yin garkuwa da fitaccen Malamin addini a jihar Sheikh Adam Al-Garkawy akan hanyarsa ta zuwa gona.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mukhtar Aliyu, ya tabbatar da faruwar wannan lamari a wata sanarwa da ya fitar a jihar Kaduna.

An sace Sheikh Al-Garkawy ne akan hanyarsa ta zuwa gona a ranar Alhamis tare da wasu mutum biyu tare da shi, wadan da dalibansa.

An dai sace Al-Garkawy ne akan hanyarsa ta zuwa gonarsa dake kauyen Maguzawa a yankin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

 

LEAVE A REPLY