Dakuku Peterside

Daga Hassan Y.A. Malik

Wasu ‘yan bindiga da suka yi shigar mata sun sace mahaifiyar daraktan hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta kasa NIMASA, Gambo Mahuta tare da wata mata.

‘Yan bindigan sun sace matan ne Hajiya Duduwa (mahaifiyar daraktan NIMASA) da Haijya Aisjha a gidan iyalan Ahmed Mahuta da ke Malumfashi.

Rahotanni sun bayyana cewa daga baya ‘yan bindigan sun sako Hajiya Aisha a yayin da suka gane cewa ba isashen lafiya ke gare ta ba amma sai suka tafi da ‘yar ta Hajiya Duduwa.

An gano cewa Hajiya Aisha ta kasance mahaifiyar tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INCE na yankin, Hussaini Mahuta.

Wata mijiya ta fadawa manema labarai cewa ‘yan binidgan sun yi shigar mata ne sanye da hijabi a yayin da suka kai harin a gidan da ke unguwar Tudun Balan Maiduna a garin Malumfashi da misalin karfe 10 na daren Litinin.

An kuma gano cewa ‘yan bindigan sun tuntubi iyalan wacce suka sace inda suka bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan N300 kafin su sake ta.

Manema labarai sun yi kokarin su tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina, DSP Gambo Isah, amma bai daga waya ba duk da tarin kiran da aka yi masa.

LEAVE A REPLY