‘Yan sanda a ranar Alhamis sun gabatar da Maryam Sanda da mahaifiyarta Maimuna Aliyu da dan uwanta Aliyu Sanda da kuma wata budurwa Sadiya Aminu akan zargin da ake yi musu kan kisan Bilyaminu Bello.

Shi dai Bilyaminu Bello da ne a wajen tsohon Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Bello Halliru Mohammed.

Wadan da ake zargin sun gurfana a gaban babbar kotun Abuja dake zamanta a Jabi, akan zargi guda biyu da ake yi musu na; hada baki yayin da aka kashe Bilyaminu Sanda domin kawar da shaidun da zasu fayyace gaskiya abin.

Lauya da yake kare wadan da ake tuhuma, Joseph Dawodu ya nemi da kotu ta bayar da belin mutanan da yake karewa, a wata takarda da ya rubuta mai shafi 18 da yake neman kotu ta bashi belinsu, hade da takardun asibiti da suke tabbatar dacikar sharuddan bayar da belin, tare da rokon kotun tayi la’akari da jaririyar ‘tar wata 8 da ita Maryam Sanda take shayarwa.

Sai dai kuma, lauyan masu gabatar da kara ya kalubalanci amfani da jaririyar maryam Sanda a matsayin wani dalili da zai sanya a bayar da belin wadan da yake kara.

Kotu dai ta daga batun bayar da beli har sai zuwa nan da 3 na yammacin ranar Alhamis din, domin yanke ko zata bayar da belin ko kuma a’a.

LEAVE A REPLY