Daga Abba LG Gwale

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zargi marigayi tsohon shugaban kasar Libiya, Mu’ammar Gaddafi da bai wa makiyaya makamai a yankin Yammacin Afirka.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya aike wa da manema labarai inda yace matsalolin yawaitar makamai hannun farar hula laifin marigayin ne.

Sanarwar ta kunshi bayanan da shugaban ya yi wa Archbishop na Canterbury,mai suna Justin Welby, a kan dalilinsa na son sake tsayawa takara karo na biyu a ganawar da suka yi a birnin Landan din kasar ingila

Mista Buhari ya kuma bayyana wa Mista Welby cewa rikicin manoma da makiyaya tsohon abu ne da aka dade ana fama da shi a kasar nan sai dai a yanzu lamarin ya yi muni ne saboda yadda ‘yan bindiga daga yankin kudu da hamadar sahara ke kara kutsawa cikin yankin Yammacin Afirka

Shugaban  ya kara da cewa Mu’ammar Gaddafi na Libiya ne ya horar da wadannan ‘yan bindiga sai dai kuma  da aka kashe shi sai suka tsere da makaman dake hannunsu

Yaci ga da cewa kasar nan taga ire-irensu a yakin da take yi da qungiyar Boko Haram inda yace  makiyaya da a lokutan baya  aka sansu da daukar sanda ko lauje don gyara hanyar wucewarsu kawai, amma na yanzu su na daukar mugayen makamai.

Buhari  ya kuma bayyanawa Archbishop na Canterbury  matsalar rikicin manoma da makiyaya ba abun da ya shafi addini ba ne, lamari ne da ya shafi zamantakewa da tattalin arziki.

Ya kuma koka da cewa siyasa marar kan gado ce ta jawo rikicin manoma da makiyaya, amma ya bayar da tabbacin samar da mafita ta din-din-din.

A bara, gwamnatin Najeriya ta sanya dokar hana kiwo a wasu yankunan kasar wacce ta jawo ce-ce-ku-ce, inda ta ce a dinga killace shanu a waje daya.

Sai dai kuma an yi biris da wannan doka kuma ana ci gaba da samun rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a fadin kasar nan.

LEAVE A REPLY