Mai Tallafawa Gwamnan Jahar Bauchi kan kungiyoyin da bana Gwamnati ba da abokan kawo cigaba, Mallam Mansur Manu Soro ya biya ma dukkan fursononi da ake bi bashi ko tara a gidan kaso na Darazo.

Mallam Mansur yace yayi hakan ne don neman gafarar Allah cikin wannan kwanaki na “Ayyamul Tashrik”masu alfarma.

Shugaban gidan kaso na Darazo Muktar Muhamad ya nuna jin dadinsa matuka ya kuma yi kira ga wadanda suka samu ‘yantawar su zama masu kiyaye doka da oda.

Shugaban jamiyyar APC na karamar hukumar Darazo Danjuma Mohammed yayi adduan samu lada da nasara a zaben 2019 wa Hon Mansur Manu Soro.

 

LEAVE A REPLY