Kwamishinan Ilimin jihar Nasarawa, Aliyu Tijjani ya bayyana cewar ruwan sama kamar da bakin kwarya yayi sanadiyar rushewar makarantun Gwamnati 35 a fadin jihar Nasarawa.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a ranar Laraba a Lafiya babban birnin jihar Nasarawa.

Ya bayyana cewar mamakon ruwan saman ya lalata makarantun ne a dukkan sassan jihar a kananan hukumomi 13 dake fadin jihar.

A cewarsa, ambaliyar ruwan tafi shafar karamar hukumar Doma tun bayan wani ruwa da aka shatata a ranar 8 ga watan Mayu wanda ya shafi makarantu 12 dake yankin.

“Tuni muka kafawani kwamaiti da zai zagaya inda abin ya faru domin bamu kididdigar irin hasarar da aka yi a sanadiyar wannan ruwan sama kamar da bakin kwarya”

“A halin yanzu Gwamna baya nan, amma daga zarar ya dawo za a shiga aikin gyaran makarantun gadan gadan” A cewar Kwamishinan Ilimin jihar.

LEAVE A REPLY