Daga Hassan Y. A. Malik

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da kama bindigu 60 da alburusai masu tarin yawa, wadanda aka mallake su ba bisa ka’ida ba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar ta tashi tsaye wajen ganin ta hana mallakar makamai ba bisa doka ba a fadin Nijeriya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Rabiu Musa, shi ne ya bayyana hakan a yayin da yake nuna bindigun ga manema labarai a Kano a jiya Laraba.

Musa ya ce daga cikin makaman da aka kama akwai manyan bindigu kirar rifle guda 37 da kanana kirar Pistol guda 23 da sauransu, da kuma alburusai da dama.

Ya ce mafiya yawan makaman an same su ne bayan da masu su suka mika su ga jami’an tsaron hadin gwiwa a karan kansu.

Kwamishinan ya kara da cewa hakan ya biyo bayan umarnin da Sufeta Janar na ‘yan sanda, Ibrahim Idris, ya bayar na kokarin bankado haramtattun makamai a mafi yawan jihohin Nijeriya.

A karshe, ya yi kira ga duk mai haramtaccen makami da ya mika nasa, inda ya ce duk wanda aka kama zai fuskanci fushin hukuma,  ya kuma roki jama’a da su kai rahotan duk wanda suka gani da makami.

LEAVE A REPLY