Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau
Umar Farouk Muhammad
A ranar 12 June, 2018  kotu ta zauna domin sauraren bukatar da lauyan Mallam Ibrahim Shekarau ya gabatar a gaban mai shari’a Hajiya Zainab Bage Abubakar  inda lauyan ya nemi a baiwa Sardaunan Kano fasfo dinsa don yaje aikin Umrah, mai shari’a Zainab taki amincewa da wannan bukata inda tace rike wannan fasfo yana daga sharudan belin da ta bayar, ta kuma tabbatar wa da lauya Barrister Abdul Fagge cewa shari’a tana nan za a cigaba da sauraren ta ranar 26 June, 2018 a kotun ta dake zama a Court Road Kano.
Ana tuhumar Mal Ibrahim Shekarau da karbar  #25M daga kudin zaben 2015 da Jam’iyyar PDP ta aiko jihar Kano.
Mal Ibrahim Shekarau ya rike Gwamnan kano shekaru takwas , bayan saukar sa anyi bincike ba a same shi da Almundahana ba.
Haka kuma ya rike ministan ilimi na wata 10 nan ma bayan saukar sa an bincike shi ba a same shi da wani laifi ba, harma kwamitin binciken ya gano Mallamin bai biya kansa alawus din sa ba, daga kashe kwamitin ya bada umarni a biya shi alawus din.
Wannan mutum yau shi gwamnati ke tuhuma da karbar #25m daga kudin zabe, kudin zaben da ya musanta karba kuma ya nemi a kawo hujjar da zata nuna ya karba din, duk da an rasa hujjar amma aka mika shi kotu.
Za mu ci gaba da bibiyar Shari’ar mu ga yadda za ta kasance, fatanmu dai masu Shari’a su ci gaba da aikin su a matsayin masu zama da kafafun su, tunda su ka daine hukumar da basu zama ‘yan amshin shatar APC ba.

LEAVE A REPLY