Alhaji Lai Mohammed

Babbar kotun tarayya dake Legas ta bayar da umarnin a kaiwa ministan yada labarai da al’adu na tarayyar Najeriya Alhaji Lai Mohammed sammaci kan batun sunayen da yace na barayin kudin Gwamnati ne ya fitar.

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar, babbar kotun tarayya dake birnin Fatakwal na jihar Ribas a ranar Laraba 28 ga watan Afrilu, inda take tuhumarsa kan bayyana sunan Uche Secondus, shugaban jam’iyyar PDP na kasa a cikin jerin sunayen barayi.

Alkalin kotun, mai shari’ah Adama Iyayi-Lamikanra, ita ce ta bayar da umarnin kaiwa ministan sammaci, inda take tuhumarsa da sanya sunan Uche Secondus cikin jerin sunayen barayin kudin Gwamnati inda tace ya karbi Naira miliyan 200 a ranar 19 ga watan Fabrairun 2015 daga ofishin Sambo Dasuki.

 

LEAVE A REPLY