Zauren Majalisar Wakilai ta tarayya

Majalisar dokoki ta tarayya zata binciki badakalar sayar da kamfanin samar da wutar lantarki na kasa PHCN da batun asarar Naira biliyan 2 da kuma dala miliyan 3.8 na kudin ruwa da aka yi.

Wannan kuduri na binciken ya biyo bayan amincewa da ‘yan majalisar baki daya suka yi na kudurin da dan majalisa Chukwuka Onyema daga jihar Anambara ya gabatar a zauren majalisar a ranar Talata.

Kakakin majalisar dokokin Yakubu Doga ya buga gudumar amincewa da wannan kuduri bayan da ‘yan majalisar suka mince a yi wannan bincike.

Majilsar dai ta amince ta kafa wani kwamiti wanda zai jagoranci wannan bincike, sannan ya dawo da rahoton binciken a cikin sati shida, domin daukar mataki na karshe kan batun.

Mista Onyema ya bayyana cewar, kamfanoni guda shi ne suka saye PHCN din yayin da kamfanoni guda 12 suke aikin rarraba wutar lantarkin ga jihohin Najeriya 36 har da Abuja.

Dan majalisar ya ce akwai lauje cikin nadi a cefanarda kamfanin rarraba wutar lantarki na PHCN da aka yi, dan haka dole a binciki yadda lamuran suke.

Yace kamfanonin da aka ce sun ci nasarar sayan kamfanin sun biya kudade ne ta Bankunan Standard Chartered Bank da Fidelity Bank da Stanbic IBTCda Access Bank da FCMB da Skye Bank da Sterling Bank da Zenith Bank da kuma Bankin Unity.

Yace an karkatar da akalar kudaden da suka kai Naira biliyan 2 da kuma dalar Amurka miliyan 3.8 daga ainihin asusun Gwamnatin tarayya zuwa aljihun wasu mutane daban, anyi haka ne kuma tare da hadin bakin bankunan da kuma ma’aikatan babban Bankin kasa CBN. A cewar Mista Onyema.

Ya bayyanar da cewar, kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa majalisar dokoki ta kasa ‘yancin bincikar wannan cciniki mai cike da badakala, domin bankado muguwar almundahanar da aka tafka.

NAN

LEAVE A REPLY