Hon. Abdulmumin Jibril Kofa

Majalisar dokoki ta tarayya ta dage dakatarwar da ta yiwa dan majalisa mai wakultar kananan hukumomin Kiru da Bebeji a majalisar wakilai ta tarayya.

Wannan dage dakatarwa ta biyo bayan wata wasika da Hon. Abdulmumin Jibrin ya rubuta kuma ya sanya hannu, yana mai neman afuwar majalisar wakilai akan laifuffukan da yayi a baya.

Kakakin majalisar Yakubu Dogara shi ne ya karanta wani sashi na wasikar  da Jibriln Kofa ya aikowa da majalisar, inda Dogara ya bayar  da sanarwar yi masa afuwa bisa cewar ya cika dukkan umarnin da aka gindaya masa.

Tun a shekarar 2017 ne majalisar ta dakatar da Jibril Kofa na tsawon kwanaki 180, bayan tonon sililin da yayi na cewar anyi cushe a cikinkasafin kudi, abinda ya janyo zazzafar muhawara a najeriya.

Dakatarwar da aka yiwa Jibril Kofa ta haura kwanakin da aka deba masa na 180 inda ya kusan shekara guda a matsayin dakataccen dan majalisar wakilai.

LEAVE A REPLY