Babbar kotun jihar Kano ta bayyana cewar majalisar dokokin jihar Kano ba ta da hurumin bincikar bidiyon badakalar Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yana karbar cin hanci daga ‘Yan kwangila.

Da yake bayyana hukuncin kotun, Mai Shariah AT Badamasi ya bayyana cewar laifi ne da ya sabawa sashi na 115 da kuma 116 a kundin tsarin mulki, amma kuma majalisar dokokin ba tada hurumin bincikar Gwamna nai ci.

Ya Kara da cewar, binciken manyan laifuka irin wannan aiki ne na hukumomin Gwamnati da suke aikin bincike irin wannan kamar EFCC da ICPC ko kuma rundunar ‘Yan sanda.

Ya kamata ace tun farko jaridar Daily Nigerian ta mika wadannan bidiyoyi zuwa ga hukumomin da ya dace.

 

LEAVE A REPLY