Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali

Majalisar dokokin jihar Zamfara zata aika waska ga ministan tsaron najeriya, Mansur Dan-Ali kan batun halin da tsaron jihar yake ciki, inda ake kashe mutane babu kakkautawa a yankunan karkara a jihar.

Majalisar dai zata nemi ministan ya kaiwa jihar Dauki kasancewwar halin da take ciki ana kai mata hare haren ‘yan ta’adda babu ji babu gani, inda ake kashe mutane da dama a kauyukan jihar.

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Maru Abdullahi Dansadau shi ne ya rubuta gabatar da wannan kuduri gaban zauren majalisar dokokin jihar, kan yadda ake ta kaiwa jihar hare hare, an kuma kasa daukar matakin hanawa.

Dan majalisar yace akwai abin takaici kwarai yadda aka yi sakaci mutane suke mutuwa ba tare da sun sanlaifin da suka yi ba aka kashe su.

Kusan baki dayan ‘yan majalisar dokokin jihar sun amince da wannan kuduri na neman karin bayani daga Ministan tsaron Najeriya dan jin bayanin yadda halin tsaro yake ciki a jihar, da kuma neman a kara musu yawan jami’an tsaro a jihar.

LEAVE A REPLY