Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal

Gwamnan jihar Sakkwato, AMinu Waziri Tambuwal a ranar Talata ya amince da nadin Umar Dodo a matsayin sabon Akawun majalisar dokokin jihar.

Gwamna Tambuwal ya bayyana cewar, nadin da aka yiwa Umar Dodo yana cikin tanade tanaden dokokin hukumar dake kula da shanin ayyukan majalisar jihar.

Ya kara da cewar, tuni aka turawa sabon Akawun majalisar wasikar amincewa da nadin nasa.

DAILY NIGERIAN ta habarto cewar, nadin sabon Akawun majalisar ya biyo bayan rasuwar tsohon Akawun majalisar ne Sulaiman Muhammad, wanda ya rasu a ranar 29 ga watan Mayun 2017.

Daman kuma, Umar Dodo shi ne mataimakin tsohon Akawun majalisar.

NAN

LEAVE A REPLY