Majalisar dokokin jihar Kano a ranar Litinin ta ce zata sauya fasalin dokar  da ta tanadi biya tsaffin Gwamnoni da mataimakansu fansho da garatuti bayan sun bar ofis.

Majalisar ta dauki wannan aniya ne a sakamakon wani kuduri da da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Warawa, Labaran Madari ya gabatar a gabanta.

A cewar dan majalisar, sauya fasalin dokar ya zama dole domin rage yawan biyan kudade na babbu gaira babu dalili ga tsofaffin Gwamnoni da mataimakansu, wanda galibi suna samun wasu ofisoshin da suke samun albashi bayan sun bar Gwamna.

Mista Labaran yace, yin wannan fasali ya biyo bayan halin matsin tattalin arziki da kasarnan ta auka ciki, a cewarsa bai dace a dinga diban kudaden al’umma ana baiwa wasu mutane suna cin albashi tudu biyu ba.

Danmajalisaryace duk wani mataimakin Gwamna da ya zama Gwamna shima dole a dakatar da biyansa fansho, domin babu yadda za’a ce mutum yana samun albashi a matsayin Gwamna, sannan kuma yana samun fansho a matsayin tsohon mataimakin Gwamna.

“A matsayinmu na wakilan jama’a, hakkinmu ne mu samar da hanyar da za’a rage yawan kudaden da ake baiwa wadan da suka bar mulki, domin ragewa Gwamnati nauyi, domin ta samu ta aiwatarwa da al’umma ayyukan da suka dace” A cewar dan majalisar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar, ‘yan majalisar dokokin jihar Kanon karkashin Kakakin Majalisa Abdullahi Ata, sun bukaci a kafa wani kwamiti na musamman da zai duba wannan batu.

Majalisar ta kafa wani kwamiti karkashin mai tsawatarwa na majalisar, Kabiru Hassan-Dashi, an kuma baiwa kwamitin sati biyu domin ya kawo rahoto.

NAN

LEAVE A REPLY