Majalisar dattawa a ranar Talata ta yi Allah wadai da abinda ya faru na rikicin addini tsakanin Musulmi da Kirista a kasuwar Magani a yankin karamar hukumar Kajuru dake jihar Kaduna.

Haka kuma, Majalisar ta yi kiran da a rungumi juna a zauna lafiya tsakanin kabilu da bangarorin Musulmi da Kirista.

Hakan ya biyo bayan maganar da Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya kawo gaban majalisar inda ya nemi majalisar ta ja hankali.

Sanata Shehu Sani ya bayyana kashe kashen da cewar abin tur da Allah wadai da rashin sanin ciwon kai.

Haka kuma, Sanatan ya nemi a zauna lafiya a yi hakuri da juna, yace bai kamata mutane su dinga kone dukiyoyinsu da suka sha wahalar tarawa ba.

Ya bayyana cewar, sabani tsakani Musulmi da Kirista abu ne da za’a iya warware shi akan tebur ba tare da tashin hankali ko hatsaniya ba.

“Ya zama dole mutane su koyi yadda zasu zauna da juna lafiya” A cewar Sanata Shehu Sani.

Mataimakin SHugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu yayi kira da a zauna lafiya da juna tsakanin ‘yan Najeriya”

 

LEAVE A REPLY