Marigayi Cif MKO Abiola

Majalisar dattawa a ranar Alhamis ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya umarci  hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC da ta fitar da sakamakon zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993 na Shugaban kasa, wanda ake ikirarin cewar Moshood Abiola ne ya lashe.

Haka kuma, majalisar ta yabawa Shugaban kasa kan yadda ya ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Demokaradiyya a Najeriya, da kuma lambar girma ta kasa mafi girma ta GCFR da aka baiwa Abiola da mataimakinsa Babagana Kingbe da ya samu GCON.

 

LEAVE A REPLY