Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki

Shugaban majalisardattawa, Bukola Saraki a ranar Litinin ya bayyana cewar majalisa ta takwas da yake jagoranci ta aiwatar da kudurori guda 213 tun daga watan Yunin shekarar 2015 zuwa yunin shekarar 2018.

Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya  fitar a ranar Litinin a birnin tarayya Abuj. Yace wannan gagarumar nasara da majalisar ta samu karkashin, ta samu ne sakamakon goyon bayan ‘yan Najeriya da suka samu.

A sanarwar da Yusuf Olaniyonu, babban mai taimakawa Shugaban majaisar akan hulda da kafafen yada Labarai ya fitar, Saraki yakara da cewar, “mun aiwatar da kudurori 213tare da zartar da kwantan guda 138 da muka gada daga majalisar da ta gabata, wanda dukkansu al’umma ne suka aiko da su”

 

LEAVE A REPLY