Daga Hassan Y.A. Malik

Wani magidanci mai suna Adamu Dewa ya gamu da ajalin sa a jiya Talata a yayin da ya ke yunkurin raba matansa biyu da suka kacame da kokuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa daya daga cikin matan na Adamu Dewa ce ta daba masa wuka, inda a take ya ce ga garin ku nan.

Wannan mummunan lamari dai ya faru ne a Dirdeu da ke jahar Adamawa.

Wani ganau, Abdulrahman Njidda Yebb ya bayyana cewa uwargidan Dewa wacce ya aura shekaru 20 da suka gabata ita ta daba masa wukar.

Rahotanni sun bayyana cewa uwargidan wacce ke da ‘ya’ya 5 da shi, dama ta sha yi masa barazana a sakamakon abunda ta kira rashin adalci da ya ke mata da son kai da ya ke nunawa amaryar shi.

LEAVE A REPLY