Alh. Mansur Manu Soro a lokacin da yake jajantawa al'ummar da suka gamu da Ibtila'in gobara
Mai tallafawa Gwamna M A Abubakar a kan kungiyoyin da bana Gwamnati ba da abokan kawo cigaba Alh Mansur Manu Soro (MMS) ya kai tallafin jin kai ga al’umar garin Marbini dake Karamar Hukumar Ganjuwa da iftila’in gobara ya afka musu har gidaje kimanin talatin da dukiya ta dubban naira suka kone kurmus inda ya sadaukar da albashinsa na watanni biyu domin tallafa musu.
Alh Mansur Manu Soro wanda yayi takanas-ta- Kano zuwa garin domin ganewa idonsa barnar da gobarar tayi da kuma jajantawa ya nuna alhini da jimami ga wannan mujarrabi da ya sami al’umar Marbini.
Bayan ya zaga dukkan gidajen da gobarar ta kone ya mika gudunmawar tabarmai da kudi ga kowanne gida da iftila’in ya shafa wanda ya bayyana cewa albashinsa ne na watanni biyu ya sadaukar musu.
Ya bayyana cewa ya kadu sosai daya ji labarin masifar data auku a garin don hakane ma yaga ya zama wajibi yazo da kansa ba aike ba don jajanta musu da basu tallafi.
Da yake jawabi, Sarkin Marbini Alh Ya’u Ibrahim ya nuna matukar godiyarsa da jin dadi da irin wannan ziyara da taimakon jin kai da Alh Mansur Manu Soro ya kawo musu. Inda yace abune mai matukar wuya a irin wannan zamani mutum yayi irin wannan sadaukarwa ga al’uma. Yace sun jima suna jin labarin tausayi da taimako da mai tallafawa gwamnan yake yiwa talakawa sai gashi yau sun gani da idonsu. Yace lallai irin yadda Alh Mansur yake da tausayin na kasa dashi abin sai wanda Allah Ya zaba, don haka yayi kira da ya dore da wannan abun kirki domin irinsu basu da yawa a cikin al’uma.
Shima da yake maida jawabi a madadin wadanda gobarar ta afkawa Mallam Sa’idu Ya’u Marbini yace basu da kalmar daza ta wadatar wajen nuna godiyarsu ga Alh Mansur Manu Soro sai dai su cigaba dayi masa adduar Allah Ya saka masa da mafificin alkhairi.
 A karshe an gudanar da addu’oi na musamman ga mai tallafawa gwamnan da Gwamna M A Abubakar.
Sai dai akan hanyarsa ta dawowa Bauchi daga garin na Marbini, daruruwan mata da matasa sunyi dandazo a a garuruwan Ganjuwa,Gandu, Kafi-radi inda sukayi ta wakoki da jinjina ga Alh Mansur Manu Soro da Gwamna M A Abubakar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da daga hotunansu. A dukkan garuruwan, mai tallafawa gwamnan ya fito inda ya gana da al’uma ya kuma tabbatar musu da kudirin Gwamna M A Abubakar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na cigaba da kawo shirye-shirye domin tallafawa mata da matasa musamman ma idan suka dawo a karo na biyu. Sai dai al’umomin wadannan garuruwan sun kara jaddada bukatar da suke da ita na mai tallafawa gwamnan Alh Mansur Manu Soro ya fito takara don wakiltarsu a majalisar tarayya dake Abuja domin basu da mai kaunar talakawa kamarsa. Alh Mansur Manu Soro ya jaddada musu bashi da wani buri irin na ya taimaki al’uma don haka ya nan yana nazarin kiraye-kirayensu kuma bazai basu kunya ba.

LEAVE A REPLY