Mai Tallafawa Gwamnan Bauchi akan Kungiyoyin Da Bana Gwamnati ba da Abokan Kawo Cigaba Alh Mansur Manu Soro ya dauki nauyin gyaran famfunan tuka-tuka a garin Nabayi da Dabe da kuma gayaran famfo mai amfani da hasken rana a garin Soro duk a Karamar Hukumar Ganjuwa.
Wannan ya biyo bayan rahoton daya samu na lalacewar famfunan wanda hakan ya jefa al’umar yankunan a cikin halin ni-‘yasu wajen samun ruwan da zasuyi al’umaran yau da kullum. Hon Mansur Manu Soro ya tausaya matuka da halin da jama’a ke ciki inda ba tare da bata lokaci ba ya sayi dukkanin kayayyakin da ake bukata wajen aikin na dubban Nairori ya kuma tura masu gyara domin fara aiki ba tare da bata lokaci ba.

LEAVE A REPLY