Babban manajan darakan babban kamfanin main a kasa Mai kanti baru ya maida martini kan zargin da karamin ministan manfetur Ibe Kachikwu yayi masa kan rashin bin ka’ida wajen fitar da kwangiloli. Karamin ministan dai ya kai Baru kara ne wajen shugaban kasa kuma mai rike da kujerar babban ministan mai na kasa Muhammadu Buhari, kan abinda yake cewa, Baru baya bin ka’ida wajen bayar da kwangiloli a ma’aikatar mai ta kasa.

A wata sanarwa da kakakin NNPC Ndu Ughamadu ya rabawa manema labarai a ranar litinin, yace zargin da akaiwa Mai-kanti Baru zargi ne mara tushe balle maka, yace, a ko da yaushe Baru yana bin ka’ida wajen bayar da ko wace irin kwangila.

Yace dukkan wasu ayyuka da aka fitarda su, musamman na Ajakouta – Kaduna – Kano da kuma NPDC duk anyi su bisa kan dokoki da ka’ida wajen bayar das u.

LEAVE A REPLY