Daga Hassan Y.A. Malik

Wata budurwa mai shekaru 18 ta zayyanawa  kotu yadda mahaifinta ya yi ta lalata da ita tun lokacin da ta ke ‘yar shekaru 12.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa an gurfanar da mahaifin mai shekaru 52, Folorunsho Oluwaseun a kotu a ranar 8 ga watan Fabrilu a bisa zargin sa da laifuka biyu da suka hada da fyade da cin zarafi.

Da ta ke fadawa kotun wacce ke zama a Ikeja a jahar Lagos yadda abun ya faru, matashiyar ta ce lamarin ya faru tsakanin shekarar 2012 zuwa 2016 a lokacin da ita da kannenta biyu ke zaune da baban na su a gidan shi da ke Ikorodu a jihar Lagos,ita kuma mahaifiyarsu ta na Ibadan saboda sun rabu da mahaifin.

Ta ce a lokacin da abun ke faruwa, a duk lokacin da ta ki yarda da mahaifin sai ya hana ta da kannenta biyu masu shekaru 2 da 5 abinci. Ta ce idan yunwa ta ishe su, babu yadda za ta yi sai kawai ta yarda.

Wannan mummunan lamari ya ci gaba duk da cewa matashiyar ta fadawa kanwar mahaifinta abun da ke faruwa, har sai da wata rana da mahaifiyar ta zo gidan ganin su ta kuma kama mahaifin hannu dumu dumu.

Yarinyar ta ce daga nan ne mahaifiyar ta kwashe su ta koma da su Ibadan gudun kar mahaifin ya kashe ta bisa abun da ta sani.

A Ibadan, matashiyar ta fara aiki a wata makaranta, inda daga bisani ta fadawa shugabar makarantar duk abunda ya faru tsakanin ta da mahaifin ta, inda ita kuma ta taimaka wajen kai batun gaban hukuma.

Laifin da Oluwasuen ya aikata dai ya saba da sashe na 137 da na 263 na kundin dokar jahar Lagos.

Alkalin kotun, Sybil Nwaka ya daga sauraran karar zuwa ranar 21 ga watan Yuni.

 

LEAVE A REPLY