Madatsar ruwa ta Kangimi dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna

Unguwanni kusan shida dake da iyaka da Madatsar ruwa ta Kangimi a yankin karamar hukumar Igabi dake jihar Kaduna, sun koka kan yadda Gwamnatin jihar ta kasa daukar mataki kan madatsar ruwan dake kusa da su, sabida tana dab da ballewa.

Mutanan sun bayyana, a wata sanarwa da suka rabawa manema labarai, sunce babbar katangar madatsar ruwan ta nuna alamun tsagewa tun cikin watan Octobar 2017.

Sanarwar wadda Usman Jikan-Mudi ya sanyawa hannu tace, dubban al’ummar dake makwabtaka da madatsarruwan, yanzu duk suna zaune cikin tsoroda fargaba, domin ana iya samun ambaliyar ruwa a koda yaushe a yankin.

“Idan kuka kalli inda wata tsawa mai karfi ta haifar da wani tsagewa a jikin katangar,zaku ga cewar lallai ruwa yana fitowa waje daga cikin ainihin madatsar, har ma an fara samun ciyayi suna fitowa a wajen, matukar ba’a dauki mataki ba, to wajen na iya budewa a ko da yaushe”

Ya bayyana garuruwan da suke fuskantar wannan baranar kamar Gobirawa, Ruhogi, Barkonu, Cikaji, Unguwar Yamman Likoro da kuma Girkawa.

“Akwai dubban mutane da suke makwabtaka da wajen, iyalansu duk suna cikin mawuyacin halin cewar wannan waje ka iya ballewa a ko da yaushe”

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya tabbatarwa da al’ummar  cewar gwamnati zata yi wani abu akai cikin gaggawa, a lokacin da yake karbar korafin al’ummar wajen a madadin Gwamnan jihar, Sa’idu Adamu mai taimakawa Gwamnan jihar kan sadarwa.

“Gwamnan jihar Kaduna zai duba wannan koke cikin gaggawa,kuma ina tabbatar muku cewar, Gwamnatin Kaduna zata yi abin da ya dace kan wannan matsalar” A cewar Sa’idu Adamu.

NAN

LEAVE A REPLY