Fiye da watanni 17 ne ma’aikatan Gwamnatin jihar Oyo suke bin Gwamnatin jihar bashin albashinsu, a sabida haka ne, kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Oyo ta shiga wani yajin aikin gargadi na kwana uku a ranar larabar nan.

Wannan umarni na shiga yajin aikin ya zo ne bayan da wata sanarwa da Kofo Ogundeji da Falegbe Mayowa shugabannin kungiyoyin NLS da TUC suka sanyawa hannu da kuma Olabode Akinfenwa na kungiyar JNC.

kungiyoyin sun bayyana cewar, sunyi hakan ne domin kira ga Gwamnatin jihar da ta shiga  taitayinta, musamman ganin ma’aikatan manyan makarantu suma suna yin yajin aikin kusan makonni 13 a dalilin ma’aikata 256 da aka sallama.

Shugabanni suka bayyana cewar, an baiwa ma’aikata umarnin zaman dirshen a gidajensu na kwana uku ko Gwamnati zata ji kokensu.

Mista Olojede ya bukaci Gwamnatin jihar da ta yi amfani da kunnuwan basira ta saurari ma’aikatanjihar.

Tuni dai manya manyan jami’an Gwamnatin jihar suka shiga tattaunawa kan wannan batun yajin aikin da ma’aikatan jihar suka tsunduma.

 

LEAVE A REPLY