Gwamnan jihar Bayelsa Sereike Henry Dickson
Daga Hassan Y.A. Malik
An kama wani ma’aiakcin gwamnatin karamar hukuma da ke karbar albashin ma’akata 300 rigis a duk watan duniya.
Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson ne ya bayar da umarni da a kama wannan ma’aikaci mai ci da gumin gwamnati.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan al’umma, Daniel Iworiso-Markson ne ya bayyana hakan a jiya Litinin a wani taro na inganta tsarin da yanayin aikin ma’aikatan gwamnatin jihar da aka gudanar a babban birnin jihar, Yenagoa.

A cewar kwamishinan, wnda bai bayyana sunan ma’aiakacin ba, ya ce, ma’aikacin da aka samu da wannan aika-aika yana aiki na da saashen kudi a wata karamar hukuma da ke a yankin tsakiyar jihar.

An dai kama wannan ma’aiakaci ta hanyar tantance ma’aikata da aka gudanar a karamar hukumar, inda tantancewar ta nuna ma’aiakcin na daukar daruruwan miliyoyin Naira a kowace shekara.

“Wannan fa a karamar hukuma daya kenan. Haka kuma a kamfanin sufuri na jihar Bayelsa akwai akalla direbobi mutum 180 da ke daukar albashi, amma kwata-kwata kamfanin motoci biyar ne da shi,” inji kwamishinan.

LEAVE A REPLY