Hassan Y.A. Malik

Gamayyar limaman darikar Katolika ta Nijeriya, CBCN, ta yi allawadai da kunshin kudirin da ke gaban majalisar tarayya ya ke jiran zama dokar kasa na daidaiton jinsi da damammaki tsakanin maza da mata da a turanci a ke kira da “Gender and Equal Opportunities Bill.”

Wannan ya biyo bayan samun kunshin kudirin da suka yi dauke da wasu sadarori da ka iya zama barazana ga iyalintaka.

Haka kuma malaman sun koka da tsarin nan da ya fara zama ruwan dare a Nijeriya na bin makarantu ana rarraba musu kwaroron roba.

A sanarwar da CBCN ta fitar a yau din, limaman na darikar Katolika sun ce, “Kodayake dai mun yi amanna da bangaren kudiri da ya bukaci da a bawa mata daraja da kimar da ta dace da su, a kuma daga martabarsu, amma duk da haka, bamu gamsu da wani bangare na kudirin ba wanda ya ke zai zama barazana ga zaman lafiyar iyali.”

“Haka kuma mun yi allawadai da yanayin yadda ake rarraba kwaroron roba ga matasa a makarantunmu da sansanonin ‘yan bautar kasa na kafatanin kasar nan har ma da cibiyoyin lafiya,” inji CNCN.

CBCN, har lau ta bukaci gwamnati da ta tabbatar an rarraba katinan zabe ga duk wadanda suka yi rijista a fadin kasar daidai wa daida.

LEAVE A REPLY