Lawal Daura, tsohon Shugaban hukumar DSS

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Kanar dangiwa Umar mai ritaya ya bayyana cewar tsohon Shugaban hukumar DSS ta kasa Lawal Daura yana gudanar da wata Gwamnati ne a cikin Gwamnati.

Dangiwa Umar ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar yana mai jinjinawa mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo kan matakin da ya dauka na korar Lawal Daura daga mukaminsa na Shugaban hukumar tsaro ta DSS.

“A kusan shekara uku da Lawal Daura yayi akan mukaminsa, yana aiwatar da Gwamnatinsa ne shi kadai a cikin Gwamnatin da yake yiwa aiki, domin kuwa babu abinda yake yi sai kama karya irin tasa tare da karya dokokin hukumar tasa”

 

LEAVE A REPLY