Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed

Ministan yada labarai da al’adu na najeriya, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewar ko dan Albarkacin Noman Shinkafa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bunkasa ya dace ‘yan Najeriya su kuma zabarsa a karo na biyu a matsayin Shugaban kasa a 2019.

Lai Mohammed ya bayyana cewar wannan batu na bunkasa harkar nman Shinkafa a Najeriya, shi ne ya fitar da kasarnan daga cikin halin matsin tattalin arziki, saboda haka ya dace ‘yan najeriya su kuma zaben Shugaba Buhari dan kara bashi damar shekar hudu masu zuwa.

Ministan ya bayyana hakan ne a birnin Legas a ranar Litinin biyu ga watan Afrilu, inda yace, kaso 60 na Shinkafar da ake ci a Najeriya yanzu, anan gida aka noma, Daily Independent ta ruwaito hakan.

Ya cigaba da cewar “Bunkasa harkar nomaa Najeriya da noman Shinkafa a Najeriya ya sanya miliyoyin ‘yan Najeriya sun yi bankwana da talauci da fatara. Sabpda yanzu haka kaso 60 na shinkafar da ake ci a kasarnan manomanmu ne na gida suka noma ta”

“Kamar yadda su kansu manoman Shinkafar suke fada, batun bunkasar harkar noman shinkafa kadai ya isa ya sanya ‘yan Najeriya su kuma zabar Shugaba Buhari a matsayin Shugaban kasa a 2019”

“Muna son yin amfani da wannan damar domin yin kira ga ‘yan Najeriya, su taimaka su dinga cin Shinkafa ‘yar Najeriya domin cigaban tattalin arzikinmu”

“Tana da dadi da gardi, ga kuma karin lafiya. Bata wani daukan lokaci kafin a girbe ta”

“Shsinkafar da ake shigo mana da ita daga waje, bamu san taya ake shukata ba, bamu san yaya aka yi har ta iso garemu ba. Amma wasu bayanai sun nuna cewar galibin shinkafar da ake shigowa da ita daga waje, shekararriya ce akekawo mana ita.

“Mafiya yawan ‘yan kasashen da ake shigo mana da shinkafarsu, su basa cin irin wannan shinkafa da ake kawo mana ita. Mutanan kasar Benin ma basa cin irin wannan shinkafa. Abincin da baka san yadda aka hada shi ba, yana da matukar hadari kwarai da gaske. Ya kamata muci wadda muke iya nomawa”

“Yana da kyau ‘yan Najeriya su sani cewar, duk lokacin da suka ci Shinakafar kasar waje, suna cinye aikin da ya kamata ace ‘yan kasarsu ne suka yi. A madadin mu samarwa da mutanan kasarmu aikin yi, mu bari muna samarwa da mutanan wata kasa aikin yi”

“Yanzu ba zaku yi mamaki ba ace, a cikin shekaru uku miliyoyin ‘yan Najeriya ne suka samu aikin yi ta hanyar bunkasa harkar noman Shinkafa”

“Yana da kyau ‘yan Najeriya su sani cewar, idan suka sama masu dibar shinkafar kasar waje, to tamkar suna samarwa da mutanan Indiya da Tailan aikin yi ne, sannan suna korar ma’aikata ‘yan najeriya daga guraren aikin yinsu. Amma yanzu a kowacce jiha muna da manoman Shinkafa”

“dukkanmu muna da dangi da abokai wadan da suke manoman shinkafa ne. Idan bamu taimaka musu ba, to tamkar muna rushe musu rayuwa ne”

 

LEAVE A REPLY