Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Kungiyar fafutikar kare ‘yancin Musulmi ta MURIC, ta bayyana aniyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta raba kyautar Naira miliyan 40 ga tsaffin Shugabannin kasarnan a matsayin wani shiri na karawa masu karfi karfi.

MURIC ta bayyana hakan ne ta bakin Daraaktan kungiyar Sheikh Ishaq Akintola, wadda aka rabawa manema labarai a ranar Litinin a birnin Badun na jihar Oyo.

Kungiyar ta bayyana wannan shirin a matsayin fada da Talakawa da tsantsar nuna jari hujjanci, ta kara da cewar, wannan tsarin na mayar da mai kudi mai arzi, da kuma mayar da talaka talaka futik abin ayi Allah wadai da shi ne.

“Taya zamu yadda da kawukanmu a matsayin ‘yan kasa da, alhali akwai dubban mutanan da suka yiwa Gwamnati bauta a matsayin ma’aikata kuma suka kai munzalin ritaya,an hana su hakkinsu na tsawon Shekaru da dama, amma a bige da baiwa tsaffin Shugabanni irin wadannan makudana kudade”

“Ina tausayinmu da jin kanmu yake? inhar zamu zura ido muna gani a rabawa tsaffin Shugabannin kasa irin wannan zunzurutun kudade, bayan sun gama arzuta kansu a lokacin da suke rike da madafun iko, Gwamnatin da aka kasa biyan mafi karancin albashi na 18,000 shi ne za’a zo ana irin wannan muguwar barna da kudin?”

A cewar Akintola wannan tsabar rashin Adalci ne da nuna fifiko da wariya, kuma wannan shiri ne na kokarin fusata talakawa da matasa marasa aikin yi, da kuma daurewa cin hanci da rashawa gindi.

Yace, Gwamnati na iya yakar cin hanci da karbar rashawa, amma tilas a shigo da sauran al’umma ciki, domin guduwa tare kuma a tsira tare.

“Taya mutanan da aka kasa biya hakkinsu, aka kasa cika musu alkawrin da akai musu, ayi zaton zasu taimaka wajen yakar cin hanci a kasarnan”

“Zance na gaskiya, tsaffin Shugabanni kasarnan gaba dayansu masu arziki ne, basu wadannan makudan kudade haka siddan, zalinci ne”

Idan ba’a manta ba, a kwanakin baya, Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana cewar, Gwamnatin ta baiwa tsaffin Shugabannin wadannan kudade a madadin saya musu motocin da tun farko aka kuduri aniyar yi.

Yace a sabida haka, Gwamnati taga dacewar baiwa tsaffin Shugabannin kasar wadannan kudade idan yaso su sayi motocin da suka ga dama.

NAN

LEAVE A REPLY