Daga Hassan Y.A. Malik

Hukumar kwastam reshen Apapa da ke jihar Legas ta kama kwantenoni 4 makare da kwayar nan da aka haramta sayarwa, tramadol.

Farashin kwayoyin wanda aka shigo da su daga kasar India ya kai Naira miliyan 110.

Kwamandan rundunar hukumar na yankin, Jibrin Musa ya fadawa manema labarai a jiya Litinin cewa sun kama kwantenonin ne tsakanin ranar 6 ga watan Fabrilu da 7 ga watan Fabrilun shekarar nan.

Daya daga cikin kwantenar mai lamba MRSU 3637149 na dauke da katan din kwayoyin guda 936 mai miligram 225. Dayan kuma mai lamba MRKU 6196764 na dauke da katan din kwayar guda 368 mai miligram 120.

Kwantena ta 3 mai lamba MRSU 3516384 a dauke da katan 554 na kwayar mai miligram 120, sai kwantena ta 4 mai lamba MRKU 6058282 wacce ke dauke da katan 200 na kwayar miligram 225.

Wai kamfani mai suna Villa Gold Pharmacy daga kasar India, shi ya shigo da kwayoyin.

Musa ya ce sun cafke mutum daya yayin da suke ci gaba da bincike.

LEAVE A REPLY