Hassan Y.A. Malik

Jami’an hukumar kwastam sun yi katarin tare buhunhunan shinkafa 460 da ‘yan fasa kwabri suka yi kokari  shigo da su cikin kasar nan a cikin motar daukar man fetur.

Shugaban rudunar kwastam mai lura da shiyyar Sokoto, Kebbi da Zamfara, Nasir Ahmad ne ya bayyanawa manema labarai jiya Juma’a a jihar Sokoto.

An dai kama shinkafar ne a kan hanyar Ilela zuwa Sokoto.

Nasir Ahmad ya bayyana cewa bayan da jami’an kwastam suka fiddo shinkafar daga tankin man, shinkafar ta gurbata sakamakon mai da ya ratsa cikin buhunhunan, wanda hakan ya sa shinkafar ta zama hatsari ga lafiyar mutane.

Nasir Ahmad ya yi kira ga masu fasa kwabri da su nemi wata halastacciyar hanyar neman abinci da zai taimakawa kasa wajen inganta tattalin arzikinta.

Haka kuma ya yi kira ga jama’a da su ci gaba basu hadin kai ta hanyar tsaigunta musu masu laifi da inda masu laifin suke, don ganin sun cinma burinsu na hana shigowa da shinkafa da sauran abubuwa da gwamnati ta hana shigowa da su

LEAVE A REPLY