Tsohon Gwamnan Kano Mai neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar Shugaban Kasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a gidansa dake Yenagoa jihar Bayelsa.

Kwankwaso na jihar ta Bayelsa new kokarin da yake yi na neman goyon bayan manyan Shugabanni PDP da su marawa aniyarsa ta yin takarar Shugaban Kasa baya.

Idan ba a manta ba a baya su Kwankwaso ne suka fandarewa jam’iyyar PDP lokacin suna Gwamnoni abinda ya janyo faduwar Gwamnatin Goodluck Jonathan a zaben 2015.

LEAVE A REPLY