Daga karshe dai bayan da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kasa shawo kan Takai ya ajiye aniyarsa ta yin takarar Gwamna, inda shi Takai din yaki karbar wannan tayi na Kwankwaso. Madugun ya fito da sirikinsa a matsayin dan takararsa.

Yanzu ta tabbata Abba Kabiru Yusuf Wanda yake auren ‘yar Sanata Kwankwaso shi ne zai tsaya takara daga bangaren ‘Yan Kwankwasiyya a cikin jam’iyyar PDP.

Sai dai kuma ‘Yan Kwankwasiyya na barazanar juyawa zabin na Kwankwaso baya a fitar da sirikinsa da yayi takarar a Kwankwasiyya.

LEAVE A REPLY