Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Akalla Sanatoci guda goma sha biyar ne suka sauya sheka a zauren majalisar dattawa daga jam’iyyar mai mulki ta APC zuwa zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

A wata wasikar da aka aikewa da Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, wasikar ta tabbatar da cewar Sanatoci 14 sun sanya hannu akan takardar sauya sheka daga APC zuwa jam’iyyar PDP.

Sanatocin da suka sauya sheka zuwa PDP su ne: Rabiu Musa Kwankwaso da Barnabas Gemade da Dino Melaye da Isa Hamma Misau da Lanre Tajouso da Shaaba Lafiagi da Ubali SHittu da kuma Mohammed Shittu.

Sauran su ne Rafiu Ibrahim da Suleiman Hunkuyi da Mansurat Sunmonu da Ibrahim Danbaba da Usman Bayero Nafada da Suleiman Nazif.

Bayan da Shugaban majalisar ya karanta sunayen Sanatocin, ya kuma kara da cewar Sanata AbdulAzeez Nyako shima ya nuna aniyarsa ta komawa PDP abinda ya mayar da Sanatocin guda 15.

A dalilin sauya shekaar wadannan ‘yan majalisa, yanzu haka jam’iyyar PDP ce ke da rinjaye a zauren majalisar.

LEAVE A REPLY