Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

 

Hassan Y.A.Malik

Babbar kotun jihar Kano ta sanya ranar 8 ga watan Maris, 2018 a matsayin ranar da za ta fara sauraron karar da gwamnatin Kano ta shigar tana zargin tsohon kwamishinan lafiyar jihar a karkashin gwamnatin Kwankwaso, Dakta Abubakar Ladan Yusuf, bisa zargin yin sama da fadi da wuri na gugan wuri har Naira Miliyan 47.8.

Wadannan kudade da a ke zargin Dakta Ladan da yi n kwana da su, kudade ne da gwamnatin Kano ta ware don biyan kudin alawus-alawus da kuma kudin ruwa da wutar lantarkin da daliban jihar Kano da gwamnati ta dauki nauyin karatunsu ta kuma tura su jami’ar Mansoura ta kasar Masar.

Tsohon kwamishinan na Kwankwaso zai gurfana a gaban kotu ne bisa laifuka 3 da a ke zarginsa da gaba dayansu ke da alaka da cin hanci, rashawa da kuma handama da babakere da kudaden gwamnati.

LEAVE A REPLY