Kwamandan Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Babban Kwamandan Hisbah na jihar Kano, Sheikh AMinu Ibrahim Daurawa, ya magantu kan auren ‘yar Gwamnan jihar Kano Fatima Ganduje, wanda aka shafe mako guda ana shagulgula da kade kade da raye raye a jihar Kano.

A bikin da aka gudanar na kasaita da nuna arziki, Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya aurar da ‘yarsa Fatima ga Idris Ajimobi, dan Gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi a ranar 3 ga watan Maris a Kano.

Bikin wanda ya samu halartar Shugaban tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari da Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Gwamnonin da kuma jagoran jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya samu suka daga ko ina a musamman a jihar Kano sabida yadda aka gudanar da shi.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, wanda ita ce ta hana dukkan wasu bukukuwan da za’a yi cashiya a binar jama’a, da kuma hana cakuduwa tsakanin maza da mata a wajen bukukuwa yayin da ake kade kade da bushe bushe, ta sha suka daga mutane da dama akan wannan biki na ‘yar gidan Gwamnan Kano, inda aka gwangwaje ba tare da samun wani tsaiko daga jami’an hukumar Hisbah ba.

Sai dai kuma, bayan sati guda da tsuke bakin hukumar ta Hisbah kan wannan biki, Sheikh Daurawa ya magantu, ta hanyar bayyanawa a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewar baya gari aka yi dukkan wadancan shagulgula da ake kalubalantar hukumar Hisbah kan rashin daukar mataki akai.

Sheikh Daurawa yace “A ranar Asabar 3 ga watan Maris na bar Kano zuwa Sakkwato da misalin karfe daya na rana, inda naje Sakkwato domin yin sharhin littafin Iziyya wanda Dr. Mansur Sokoto ya wallafa”

“Bayan na yi kwana biyu a Sakkwato, daga nan na wuce kai tsaye zuwa jihar Zamfara, inda nayi wa’azi,kwana na guda a jihar na wuce Kaduna, inda na gabatar da shiri a gidan talabijin na DITV na tsawon awa biyu”

“A ranar juma’a na yiwa mata wa’azi a garin Rigasa, inda daga bisani na gabatar da hudubar Sallar Juma’a. Da magriba kuma na yi wa’azi a masallacin Sheikh Rabiu Daura”

“A ranar Asabar da safe, ina da wani wa’azin na mata a masallacin tunawa da Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, dake kaduna, daga nan ne na kamo hanya zuwa Kano. Yanzu haka ina Kano a cikin ofis dina, duk me son ganina yana iya zuwa ya gana da ni”

“Duk wanda yake son jin bahasina kan wannan biki n a’yar Gwamna yana iya zuwa ofis dina. Me kuke son nace kan wannan bikin?” A cewar Sheikh Daurawa.

LEAVE A REPLY