Hassan Y.A. Malik

Hukumomi a kwalejin ilimi mallakar jihar Bauchi da matsugunanta ke a Kangare, sun haramtawa daliban makarantar sanya duk wata nau’i ta sutura da za ta nuna tsiraici.

Jerin suturun da kwalejin ta cewa dalibanta a kul suka sanya sun hada da: dogon damammen wando da yawanci ‘yan mata ke amfani da su a wannan zamani, dan gajeren siket, da ‘yar riga mai zubin shimi da ake kira da ‘Spaghetti’, da mai dai duk wata kalar sutura da za ta bayyana tudu da gangare na jikin mace, a cewar shugaban kwalejin, Garba Kirfi.

Shugaban kwalejin ya fadawa kamfanin dillancin labarai cewa, kwalejin na dab da fitar da sabon jadawalin nau’in suturun da makarantar ta amince dalibai su yi amfani da su, tsangayar lura da harkokin dalibai ta kwalejin na aiki akan hakan.

Wasu manya a nan garin Kangare sun dauki nauyin kafa mana sambodi dauke da bayanin dokar ta yadda duk wanda ya shigo yankin zai san dokarmu, domin dai babu wanda za a bari ya shiga harabar kwalejin in har shigarsa ko shigarata ta saba da tsarin suturar da kwalejin ta fitar.

“Zuwa yanzu dai mun fara tattaunawa da kungiyoyin addinai na daliban makarantar don su wayar da kan dalibai mabiya addinai daban-daban illolin shiga mai bayyana tsiraici.”

“Kimar mutum na ga yadda ya suturta jikinsa. Wayewa ba ita ce sanya dan kamfai ki fito kina yawo a gari ba, ko kuma ka ga dalibi namiji ya sanya wando a kasan duwawunsa yana bayyana karamin wandon ya saka a ciki”

“Mun bawa tsangayoyi umarnin cewa kada su yarda dalibai su shiga aji dauka darasi, dakin jarabawa, ko dakin karatu in har dalibai bai cika dokar sutura ta kwalejin ba,” inji Garba Kirfi.

 

LEAVE A REPLY