Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufai

Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaban wata kungiya mai rajin saita tunanin tatasa ta ‘Think Right Youth Forum’ a Turance, Alhaji Sagir Baba Nationalist, ya yaba wa gwamnatin jihar Kaduna bisa ayyukan ci-gaban da ta ke yi wa al’ummominta.

Alhaji Sagir ya yi yabon ne, biyo bayan zagayen gani da idon da su ka kai domin ganin yadda aikin samar da ruwan sha na Zaria ke gudana, da aikin hanyar Dambo zuwa Soba da kuma aikin gyaran garejin ajiye manyan motocin sufuri da ke Mararrabar Jos a jihar Kaduna.

Nationalist, ya bukaci matasan Nijeriya, da su rika bibiyar ayyukan da shugabanni da wakilan al’umma ke gudanarwa da dukiyar talakawan da su ke wakiltarsu.

A karshe ya ce lokaci ya yi da ya kamata mutane su fara tunanin tsaida nagartattun mutanen da za su damka wa amana tun kafin zuwa lokacin jefa kuri’a.

LEAVE A REPLY