Uwar gidan Shugaban Najeriya, Aisha Buhari

Hassan Y.A. Malik

Kungiyar mata ta Women Connect Innitiative (WCI), ta yabawa mai dakin shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari bisa inganta rayuwar matan karkara da yara kanana da adadinsu ya kai 363,060 a cikin shekarar 2017 ta hanyar kungiyarta mai zaman kanta, wato Future Assured

Kodinatar kungiyar ta WCI, Hajiya Murjanatu Suleiman Shika ce ta bayyana hakan a wajen taron mata da kananan yara da aka gudanar a karamar hukumar Makarfi, jihar Kaduna a yau Litinin.

Hajiya Murjanatu ta bayyana bangarorin da kungiyar mai dakin shugaban kasa ta tallafawa yara kanana da matan karkara da suka hada da: ilimin yara mata, harkar lafiya, bayar da jari da koyar da sana’o’i da kuma ilimantar da yara mata da manyan mata harkar noma.

“Uwar gidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta taba rayuwar matan karkara 131,053 da kananan yara 232,007 a jihohin Kano, Kaduna, Katsina da Adamawa a shekarar 2017 kawai.”

“Wannan kyakkyawan aiki ya yi daidai da muradan da kungiyar Future Assured ta bayyana tana son ta cimma a lokacin da aka kaddamar da kungiyar a shekarar da ta gabata.”

“Wannan kokari na mai dakin shugaban kasa ta hannun kungiyarta ya nuna irin yadda mata ke da nazari da hangen nesa wajen shawo kan matsalolin al’umma in har suka samu kansu a matsayin jagoranci.”

“Nasarar da kungiyar Future Assured ta samu na mika hannun tallafi ga wannan adadi na mutane a cikin shekara guda da kafa ta ba karamin al’amari bane, kuma da zarar kungiyar ta shiga sauran jihohi, adadin mutanen da suka amfana zai kara ninkuwa.”

“Wannan namijin kokari ya sanya dole mu yabawa mai dakin shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari.” Inji Hajiya Murjanatu.

Darakan gudanarwar kungiyar Future Assured, Mr. Ihidero Victor, a nasa bayanin ya tabbatar da cewar kungiyar ta tallafawa ‘yan gudun hijira da abubuwan rage radadin rayuwa da suka hada da: kayan abinci, suturu, zannuwan gado, tabarmi, barguna kwanon rufin daki da dai sauransu.

“Sama da tirela 6 na kayan rufin daki daban-daban kungiyar ta raba ga ‘yan gudun hijira da suka rasa matsugunansu.”

“Haka kuma kungiyar ta fara ginin gidan marayu da makaranta saboda yaran da suka rasa mahaifansu da ke sansanin ‘yan gudun hijira.”

“Ta bangaren harkar noma kuwa, kungiyar ta tallafawa mata da takin zamani, da iri da irin kifi da na kajin gidan gona da kuma yadda za su samu rance don habaka harkar noma da kiwo.”

Habiba Dabo, daya daga cikin matan da suka amfana da shirin na kungiyar Future Assured ta nuna godiyarta ga Hajiya Aisha Buhari bisa abinda ta kira kokarin sauya tunanin mata da tsayar da su akan digadigansu.

LEAVE A REPLY